Bitar muhimman labaran wannan makon
Muhimman abubuwa da dama sun ɗauki hankalin jama’a a Najeriya da ma duniya baki ɗaya, a bangarori daban-daban na rayuwa.
A bangaren tsaron Najeriya, yayin da makon yake karewa ne aka samu labarain rasuwar tsohon Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, a hannun masu garkuwa da mutane.
Gwamnatin Jihar Katsina ce dai ta fitar da sanarwar cewa ciwon suga da hawan jini ne suka yi ajalin tsohon hafsan, wanda ya shafe watanni a hannun masu satar mutane don neman kudin fansa.
- An cafke mai Safarar Makamai a Kano
- Abuja: Ana cigaba da zanga-zangar tabarbarewar tsaro a Najeriya
- Ministan Tsaron Najeriya ya ce matsalar tsaro a cikin Al’umma take
A bangaren tsaron dai a wannan makon mai karewa an samu rahotannin hare-hare da sace-sacen mutane a wasu jihohi, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar ceto mutane da dama daga hannun masu satar mutane don neman kudin fansa.
Don kawo karshen wannan annoba da ta ki ci ta ki cinyewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada buƙatar haɗin kan al’umma wajen yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.
A bangaren siyasa da mulki, Shugaban Kasa Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci tare da karrama wasu fitattun ’yan Najeriya yayin bikin Ranar Dimokuraɗiyya.
Haka kuma, Majalisar Wakilai ta amince da kudiurin kafa Rundunonin ‘Yan Sanda na Jihohi, lamarin da ya jawo zazzafar muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki.
A ɓangaren tattalin arziki, rahotanni sun nuna alamun bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.
Wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna yiwuwar Najeriya ta ribaci hauhawara farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya a bana; ko da yake ya nuna damuwa cewa raunin ginshikan tattalin arziki ka iya rage hasashen da ya yi na bunkasar tattalin arzikin zuwa kashi 4.1 cikin 100 daga kashi 4.4 cikin 100 da ya yi hasashe tun farko.
Ita kuwa Gwamnatin Tarayya ta fara biyan bashin ƙananan ‘yan kwangila ne domin ƙarfafa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi.
A matakin duniya, rikicin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba da ɗaukar hankali, yayin da aka samu sabbin matakai da sauye-sauye a wasu ƙasashe da suka shafi tsaro, siyasa da tattalin arziki.
Yayin da Iran ta sanar da dakatar da tattaunawa da Amurka saboda hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a kan Lebanon da Zirin Gaza, China da Koriya ta Arewa sun kara yaukaka dankon zumuncin da ke tsakaninsu ta fukar tsaro da tattalin arziki yayin wata ziyara da Shugaba Xi Jingpin ya kai Pyongyang.
A wasanni, an samu muhimman labarai da suka haɗa da nasarorin Super Falcons, sauye-sauyen ‘yan wasa a ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa.
Sannan kuma a makon mai karewa ne aka bude Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 wadda karo na farko take gudana a kasashe uku: Amurka da Canada da Mexico.
Ko da yake Najeriya ba ta cikin gasar, ’yan asalin kasar 16 ne suke taka wa wasu kasashen leda.
A duniyar nishaɗi, auren fitacciyar jarumar Kannywood Ummi Ibro ya kasance ɗaya daga cikin labaran da suka fi jan hankalin masoya fina-finan Hausa a makon.Hotuna da bidiyon kayataccen auren sun yadu a kafofin sadarwa na zamani.
Ku ci gaba da kasancewa da blueprinthausaradio.com domin samun sahihan labarai, rahotanni da bayanai da dumi-duminsu a makon da za mu shiga.