Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya yi watsi da ikirarin cewa an bai wa Cif MKO Abiola guba, yana mai cewa rahoton binciken gawar da kwararrun likitoci daga kasashe hudu suka gudanar ya danganta mutuwarsa da ƙarar kwana.
Hakan na kunshe ne a Babi na 21 na littafin tarihin rayuwar Janar Abdulsalami Abubakar, mai shafi 264 da babi 27 mai taken ‘Call of Duty,’ wanda aka kaddamar ranar Asabar, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
An kaddamar da littafin ne domin bikin cika shekaru 84 da haihuwar tsohon shugaban ƙasar, kuma Shugaba Bola Tinubu, wanda Mataimakin sa Kashim Shettima ya wakilta ya kasance Bako na Musamman, a wajen bikin.
- Kisan Janar Rabe, biyan kananan ’yan kwangila, bude Gasar Cin Kofin Duniya
- Abuja: Ana cigaba da zanga-zangar tabarbarewar tsaro a Najeriya
Da yake rubutu kan abubuwan da suka faru kafin mutuwar Abiola a ranar 7 ga Yuli, 1998, Abubakar ya ce marigayin ya fadi ne a lokacin wani taro da wata tawagar Amurka.
Tawagar ta ƙunshi Mataimakin Sakataren Harkokin Siyasa na Amurka Tom Pickering, da Ms Susan Rice, wadda a lokacin ita ce Mataimakiyar Sakatariyar Harkokin Amurka a Afirka.
“Ban yarda cewa an baiwa Abiola guba ba. Iyalinsa sun bukaci a yi binciken gawar sa kuma mun tattaro kwararrun likitocin daga Amurka, Burtaniya, Najeriya da Kanada don gudanar da binciken. Rahoton binciken gawar ya danganta mutuwarsa da dalilai na ƙarar kwana,” Abubakar ya rubuta.
Ya kara da cewa, Abiola yana fama da wasu matsalolin lafiya da suka wanzu, ciki har da hawan jini da ciwon zuciya, tun a shekarar 1994 lokacin da aka fara tsare shi.