Babban taken da ya mamaye zanga-zangar ta ranar Asabar shi ne- “Ba za a tsorata mu ba, Rayuwar ‘yan Nijeriya tana da daraja!”
Masu zangar-zangar sun fito a ranar Asabar, kamar yadda suka fara a sauran ranakun da suka gabata, inda a yau suka tare manyan hanyoyi da ke shigewa zuwa yankunan Aya, Asokoro da tsakiyar Abuja, hanyar da akafi sani da Karu Bridge.
Daruruwan masu zanga-zangar suna kira ne da mahukuntan kasar su tashi tsaye domin yaki da abinda suka kira da wutar daji, dake yaduwa cikin gaggawa daga wani bangaren kasar zuwa saura.
An shafe tsawon mako ana zanga-zanga karkashin kungiyoyin farar hula ne, in banda Mashahuran cikin su da suka hadar da Omoyele Sowore da ke wakiltar bangaren ‘yan siyasa, da kuma Martin Vincent Otse da akafi sani da Verydarkman(VDM), a bangaren yan gwagwarmaya.
-
Allah kadai zai iya kawo karshen rashin tsaro a Najeriya – Matawalle
-
Kastina: Gwamnatin Jihar ta tabbatar da Mutuwar Janar Rabe mai ritaya
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jagoran fafutuka, Omoyele Sowore, wanda aka fi sani da gogewa wajen fuskantar mahukunta, ya jagoranci jerin gwanon matasan tare da kalubalantar matakin da jami’an tsaro ke dauka akan su.
Muryarsa ta kara ba matasan kwarin gwiwa, inda yake jaddada cewa:
“Kada ku gudu! Gwamnati tana tsoron muryarku ne shi yasa suke amfani da barkonon tsohuwa. Idan muka janye yau, rashin tsaro zai cinye mu a gidajenmu.”
A gefe guda kuma, fitaccen mai sharhi kan al’amura a kafafen sada zumunta, VeryDarkMan (VDM), halartarsa ta jawo hankalin dubun-dubatar matasa mazauna Abuja wadanda ke bibibyar sa a intanet.
VDM ya yi amfani da damar wajen daukar hotuna da bidiyoyi kai-tsaye don nuna wa duniya ainihin abin da ke faruwa, tare da yin kira ga shugabanni da su fito su amsa tambayoyin talakawa.
Fitowarsa ta tabbatar da cewa fafutuka ta shafukan sada zumunta, da kuma wadda akeyi yanzu bisa dalili na tsaro, hade su waje guda ka iya kawo masalahar da ake nema.
A ranar Juma’a, masu zanga zangar sun fuskanci fushin jami’an tsaro inda aka barbada musu barkonon tsohuwa, matakin da ake ganin shine ya sanya suka sauya fasalin fitar tasu, daga cikin Birnin zuwa kan manyan hanyoyi.
Fitowar da suke cigaba da yi, tana nuna cewa sun lashi takobin cewa ba za su janye ba har sai muryoyinsu sun kai ga hukumomi, domin fitowa su bayar da tabbacin daukar matakar gaggawa, ta dakile matsalar tsaro.
