Marigayin ya rasu ne a hannun 'yan bindiga

Gwamnatin Jihar Katsina ta Sanar da Mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar (Mai Ritaya) a hannun ‘Yan Bindiga.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron cikin gida na jihar Dakta Nasiru Mu’azu ya fitar a ranar Asabar, ta ce Janar din ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da shi.

Sanarwar tace Gwamnatin jihar tayi duk mai yiwuwa da haɗin gwiwar hukumomin tsaro don ganin an ceto shi cikin ƙoshin lafiya, amma sai dai kaddara ta riga fata.

Bayanai daga sanarwar sun nuna cewa marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka hadar da ciwon suga da kuma hawan jini, yayin da yake tsare.

Gwamnatin jihar ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da aiki kafada da kafada da Gwamnatin Tarayya, da kuma rundunar tsaro don ganin an kamo wadanda ke da hannu domin fuskantar hukuncin shari’a.

Marigayin ya shafe tsawon makonni a hannun ‘Yan Bindigar, bayan gindaya wa gwamnatin Jihar sharadin sakar musu wasu ‘yan uwa da aka kama, a matsayin musaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *