Sojojin saman Indiya biyar sun rasa rayukansu bayan jirgin da suke ciki ya yi hatsari a jihar Assam da ke arewa maso gabashin Indiya

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin saman India ta fitar, tace Jirgin nau’in Antonov An-32 mai ɗaukar kaya yayi hatsarine a yayin da yake kokarin safarar wasu kayan soji a yankin Jorhat na jihar ta Assam

Tashar talabijin ta NDTV ta nuna hotuna daga wurin hatsarin, inda aka ga  baƙin hayaki mai kauri yana tashi sama, sannan jirgin  ya karairaye zuwa sassa-sassa

Sojin saman Indiya na amfani da jiragen An-32 kusan 105 domin jigilar mutane da kaya.

Ko a shekara ta 2019 wani jirgi samfurin An-32 yayi hatsari a jahar Arunachal Pradesh, kusa da iyaka da China, inda mutane 13 suka rasa rayukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *