Wasu manyan ‘yan adawa biyu a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun samu raunuka a ranar Juma’a, yayin wata zanga-zangar adawa da shirin gwamnati na canza kundin tsarin mulki

Ƙungiyar C64 ce ta kira zanga-zanga a ranar Juma’a a gaban ginin majalisar dokoki da ke birnin Kinshasa domin nuna adawa da canza kundin tsarin mulkin.

Sai dai zanga zangar ta rikide zuwa arangama tsakanin masu zanga-zanga da masu goyon bayan gwamnati, sannan daga baya da ‘yan sanda

Shugaban ƙasa Félix Tshisekedi, mai shekaru 62, wanda ke mulki tun 2019, yana gab da kammala wa’adinsa na biyu na shekaru biyar a shekarar 2028, wanda a ƙarƙashin kundin tsarin mulki na yanzu shi ne wa’adi na ƙarshe.

Sai dai kwanan nan ya bayyana cewa zai amince ya sake tsayawa takara har wa’adi na uku “idan jama’a sun so haka” bayan kuri’ar raba-gardama kan gyaran kundin tsarin mulki.

Jam’iyyar mulki ta shafe makonni tana ƙoƙarin cire tanadin kundin tsarin mulki da ke hana shugaban ƙasa yin fiye da wa’adi biyu.

Manyan jam’iyyun adawa da ke cikin rarrabuwar kai a ƙasar sun haɗu a wata gamayya a watan da ya gabata domin adawa da abin da suke gani a matsayin yunkurin shugaban na riƙe madafun iko.

Martin Fayulu, wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2018 kuma na uku a 2023, da wani jigo a adawa mai suna Prince Epenge, sun samu ƙananan raunuka a rikicin sakamakon jifan duwatsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *