Rahotanni da dama sun ce Atletico Madrid ta tura tayin Yuro miliyan 120 (Naira biliyan 189) domin siyan Victor Osimhen, amma Galatasaray ta ki amincewa.
Atletico na neman dan wasan gaba mai gogewa saboda rashin tabbas game da makomar Alexander Sørloth (wanda ake danganta shi da Juventus) da Julián Álvarez (wanda ake danganta shi da Barcelona ko Arsenal).
Osimhen ya zura kwallaye 22 tare da ba da taimako aka ci 8 a wasanni 32, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen lashe wa Galatasaray kofin Süper Lig karo na 4 a jere.
Galatasaray ta saye shi daga Napoli kan Yuro miliyan 75 a bazarar da ta gabata, kuma kin amincewa da Yuro miliyan 120 ya nuna cewa shugabannin kulob din suna kallon darajar sa a kan Yuro miliyan 150 ko fiye.
An ruwaito cewa sauran kungiyoyi da ke sa ido a kansa sun hada da Barcelona, PSG, Man United, Chelsea, Real Madrid, da Bayern Munich.