Amurka ta fara gasar cin kofin duniya da take karbar bakunci da salo mai kayatarwa a ranar Juma’a, inda ta doke Paraguay 4-1 a wasan bude gasar da ya faranta wa ‘yan kallo rai a filin wasa na SoFi Stadiya, da ke Los Angeles.

Dan asalin Najeriya, Folarin Balogun, wanda aka haifa a birnin New York, ya zura kwallaye 2.

Matsin lambar Amurka ya tilasta wa Damian Bobadilla na Paraguay cin gida, kafin Gio Reyna da ya shigo daga benci ya kara kwallo ta hudu a karshen wasa.

Wannan nasara ce ta farko ga kocin Amurka Mauricio Pochettino a gasar, a rukunin Group D.

Amurka ta shiga gasar cikin shakku bayan rashin nasara da wasanni marasa kyau a wasannin sada zumunta da ta buga kafin gasar.

Wannan ne wasa na farko da Balogun ya zura kwallo a gasar cin kofin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *