Tawagar Ingila ta fada cikin wani babban cikas bayan an sace musu kayan aiki masu yawa gabanin wasansu na farko a gasar cin kofin duniya.

Takalman ‘yan wasa, (ciki har da na Jude Bellingham da Harry Kane), kayan atisaye, kayan aikin ma’aikatan horarwa, kwallaye da kayan sawa na ranar wasa duk an fahimci suna cikin abubuwan da aka sace, kamar yadda SkyNews ta ruwaito.

Yanzu haka sansanin tawagar Ingila na aiki tare da ‘yan sandan yankin domin gano kayan da aka sace ko kuma a samo wasu a kan lokaci domin atisaye ya ci gaba kamar yadda aka tsara.

Sai dai ‘Yan Sandan Kansas City sun ce, “An kama mutane biyu da ake zargi ana ci gaba da bincike.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *