A ranar Juma’a, kasar Canada wadda ke daya daga cikin masu karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta tashi ci 1-1 da Bosnia-Herzegovina a wasan ta na farko da ta buga a kasar Canada.
Jovo Lukic ne ya fara zura kwallo a ragar Canada da kai a minti na 21 a Toronto, sannan Cyle Larin ya farke wa Canada da aka dawo daga hutun rabin lokaci.
- Gasar Cin Kofin Duniya: Me ya sa Nahiyar Afirka ta juya wa Afirka Ta Kudu baya?
- Jadawalin FIFA: Duba matsayin Ajantina da Najeriya
Wannan shi ne karon farko da Canada ta tashi ba tare da an doke ta ba a gasar cin kofin duniya. A baya an doke ta a dukkan wasanni 3 na gasar a 1986, sannan kuma a 2022.