Ministan ya bukaci yan siyasa su daina yaudarar al'umma da batun tsaro

Karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle, ya ce Allah kadai ne zai iya kawo karshen kalubalen rashin tsaro a Najeriya.

Da yake zantawa da Sashen Hausa na BBC, Matawalle ya ce rashin tsaro ya ci gaba da zama kalubale wanda ke bukatar hadin gwiwa daga jami’an tsaro da ‘yan kasa don shawo kansa.

Ministan ya kuma gargadi ‘yan siyasa da su daina amfani da matsalar tsaro wajen cin moriyar siyasa.

Matawalle yace abin bakin ciki ne, kuma dole ne mu tashi tsaye mu tabbatar da cewa jami’an tsaro da ‘yan Najeriya sun hada kai don kawo karshen rashin tsaro a kasar.

“Allah ne kadai zai iya kawo karshen wannan rashin tsaro, tare da addu’o’inmu da kokarinmu na hadin gwiwa. Kada a yi amfani da shi domin sukar wasu ko cimma burin siyasa.” Inji Ministan

Yace rashin tsaro bashi da alaka siyasa ko addini, domin zai iya shafar kowa, a saboda haka ya bukaci ‘yan adawa da su daina amfani da rashin tsaro wajen tayar da hankalin jama’a.

A karshe Ministan ya bukaci da a daina yiwa matsalar kallon gazawar gwamnati domin cimma burin siyasa, da daina yaudarar mutane cewa su kadai ne za su iya kawo karshen rashin tsaro.

Yan siyasa a kwanakin nan na dora laifin abinda ke faruwa akan gwamnati, yayin da kungiyoyin fararen hula ke cigaba da zanga-zangar matsawa gwamnati, ta kawo karshen matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *