Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya gudanar da bikin sanya tufafi ruwan hoda a Abuja, domin wayar da kan jama’a kan cutar sankarar mama, a wani ɓangare na ayyukan tunawa da watan wayar da kai kan cutar.
Mataimakiyar Shugabar NNPC mai kula da ayyukan kasuwanci, Sophia Mbakwe, da Babban Jami’in Ayyukan Lafiya na NNPC Medical Services Limited, Dakta Dickson Bada, sun haɗu da ma’aikatan kamfanin a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026, wajen gudanar da bikin.
Shirin na da manufar ƙarfafa tattaunawa kan lafiyar mama, duba lafiyar mama akai-akai da kuma gano cutar da wuri.
- APC ta zargi Atiku da ADC da yaɗa labaran ƙarya kan taron Tinubu a Kaduna
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 15 a harin sama a Borno
An kuma buƙaci ma’aikata su ziyarci asibitocin NNPC Medical Services Limited domin a duba lafiyar mamansu.
Kamfanin ya ce za a ci gaba da ayyukan wayar da kan jama’a a ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026, ta hanyar taron ilimantarwa na intanet mai taken “Beyond Awareness: Taking Action Against Breast Cancer”, wanda Dakta Oizza Tessy Ahmadu, ƙwararriyar likitar cututtukan daji, za ta jagoranta.
Taron zai tattauna alamomin cutar sankarar mama, hanyoyin gano ta da wuri, zaɓuɓɓukan magani da wuraren samun kulawa da tallafin lafiya.