Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe ’yan ta’adda 15 a wani harin sama da ta kai yankin arewa maso yammacin Pulka, a ƙaramar hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

Rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas, mai gudanar da Operation HADIN KAI, ta ce ta kai harin ne da misalin ƙarfe 11:50 na dare ranar 23 ga Oktoba, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da tabbatar da motsin ’yan ta’adda a yankin.

Bayan harin saman, rundunar ta ce sojojin ƙasa sun shiga yankin domin gudanar da ƙarin bincike da kuma tabbatar da sakamakon harin.

Ta bayyana cewa hare-hare sun taimaka wajen tarwatsa motsin ’yan ta’addan da rage ƙarfin gudanar da ayyukansu.

Rundunar ta ƙara da cewa harin wani ɓangare ne na ci gaba da kai hare-hare bisa bayanan sirri domin hana ’yan ta’adda samun damar kai hare-hare da barazana ga al’ummomin yankin.

Ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da yaƙi da ta’addanci da tayar da ƙayar baya, tare da kare fararen hula da samar da yanayin da zai ba al’ummomin da rikici ya shafa damar komawa harkokin rayuwa da tattalin arziƙi.

Rundunar ta kuma buƙaci jama’a su ci gaba da ba jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa game da motsi ko ayyukan da suke zargi, tana mai cewa haɗin gwiwar jama’a da sojoji na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Arewa maso Gabas.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *