Bayan kammala makon farko na gasar Premier League ta 2026/27 cikin wasanni masu kayatarwa, hankali yanzu ya koma mako na 2, inda kungiyoyi za su nemi ci gaba da haskakawa, yayin da wasu kuma za su yi ƙoƙarin farfaɗowa daga rashin nasarar da suka samu.
Wasannin makon na biyu za su fara ne da fafatawar Crystal Palace da Manchester City, inda Palace za ta nemi samun maki na farko a kakar bana, yayin da City za ta yi ƙoƙarin ci gaba da samun sakamako mai kyau.
A wani babban wasa, Tottenham Hotspur za ta karɓi baƙoncin Newcastle United, yayin da Chelsea za ta kara da Brighton.
- Chelsea ta fara kakar bana da nasara, bayan doke Fulham
- Newcastle da Liverpool sun tashi kunnen doki 2–2 a St James’ Park
Chelsea da Brighton za su shiga wannan fafatawar ne da ƙwarin gwiwa, bayan da suka fara wasan makon farko da nasara.
Makon na biyu na iya zama mai muhimmanci wajen nuna kungiyoyin da za su iya ci gaba da kasancewa cikin tseren saman teburin gasar, da kuma waɗanda ke bukatar gyara kura-kuransu tun da wuri.
Ga magoya bayan Premier League, a na sa ran mako na 2 zai kawo ƙarin cin ƙwallaye da abubuwan mamaki da fafatawa mai zafi yayin da kakar 2026/27 ke ƙara ɗaukar zafi.