Rundunar haɗin gwiwar sojin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ta ce ta tare tare da lalata wani makami mai linzami kirar cruise a yankin Madina da ke yammacin Saudiyya.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Turki al-Maliki, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026, ta hanyar wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na X.
Kamfanin dillanacin labarai na Anadolu ya tabbatar da cewa rundunar ce ta fitar da sanarwar.
Sai dai, sanarwar ba ta bayyana daga inda aka harbo makamin ba, ko kuma inda aka nufa da shi. Haka kuma, ba a bayar da cikakken bayani kan ko lamarin ya yi sanadin asarar rayuka ko lalacewar dukiyoyi ba.
- An kashe mutum uku a hare-haren da aka kai filayen jiragen saman Saudiyya
-
Mutane biyu sun jikkata a harin Houthi kan yankin Jazan na Saudiyya
Lamarin ya faru ne a yayin da ake samun ƙarin hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da ke shafar Saudiyya, a daidai lokacin da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ke ƙara ƙamari.
A cikin wasu hare-haren baya-bayan nan, rundunar ta sanar da tare wasu makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a sassa daban-daban na Saudiyya.
A ranar Laraba, 14 ga Oktoba, rundunar ta ce ta lalata wani makami mai linzami da mayaƙan Houthi suka harba zuwa Riyadh, babban birnin ƙasar.
Haka kuma, a ranar Alhamis ɗin, rundunar ta sanar da tare wani jirgi marar matuƙi a yankin Gabashin Saudiyya. Sai dai, a sanarwar da ta shafi makamin da aka tare a yankin Madina, ba a bayyana wanda ya harba shi ba.
Garin Madina na daga cikin muhimman wurare masu tsarki ga Musulmi a faɗin duniya, domin yana ɗauke da Masallacin Annabi Muhammad (SAW).
Har zuwa lokacin wallafa rahoton, ba a bayyana asalin makamin, wanda ya harba shi, ko kuma inda aka nufa da shi ba.