Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da shirin rancen kuɗaɗen waje na gwamnatin tarayya na shekarun 2026 zuwa 2027, wanda ya ƙunshi dala biliyan 20.52 da Yuro biliyan 1.05 domin gudanar da ayyukan raya ƙasa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar buƙatar shugaban ƙasar yayin zaman majalisar ranar Talata.
Tinubu ya buƙaci ’yan majalisar su gaggauta duba shirin tare da amincewa da shi domin a fara aiwatar da ayyukan da aka tsara.
- FRSC ta aika allunan lambobin rajistar motoci 19,560 zuwa Abuja cikin Oktoba
- Peter Obi ya yi alƙawarin mayar da Arewa cibiyar noma da masana’antu idan ya ci zaɓen 2027
A cikin wasiƙar, Tinubu ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen wajen ayyukan more rayuwa, noma, kiwon lafiya, ilimi, samar da ruwan sha, tsaro, samar da ayyukan yi da kuma gyare-gyaren harkokin kuɗaɗen gwamnati.
Ya bayyana cewa an zaɓi ayyukan ne bayan nazarin fasaha da tattalin arziƙi, tare da la’akari da gudummawar da za su bayar wajen bunƙasa ƙasa.
Ya ƙara da cewa za a aiwatar da mafi yawan ayyukan a faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Tinubu ya ce ƙarin rancen ya zama dole saboda yawan kuɗaɗen da ake buƙata domin magance ƙarancin ababen more rayuwa a ƙasar, musamman a fannonin wutar lantarki, sufuri da kiwon lafiya.
Ya kuma ce ayyukan za su taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage talauci da inganta samar da abinci.
Akpabio ya ce za a miƙa ta ga Kwamitin Bashi na Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, tare da yiwuwar haɗa kai da kwamitocin kasafin kuɗi da kuɗaɗe domin duba cikakkun bayanai da alaƙar shirin da bashin da aka amince da shi a baya.