Sarki Charles na Ingila ya tarbi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Maidakinsa Oluremi Tinubu yayin wani biki na kasaita a Fadar Windsor da ke yamma da birnin Landan.
Wannan ne karo na farko a cikin shekara 37 da wani Shugaban Kasar Najeriyay a kai wa Masarautar Ingila ziyara irin wannan.
Daga cikin manyan da suka tarbi Shugaban Kasar akwaiMaidakin Sarki Charles, Sarauniya Camilla, da Yarima William da Gimbiya Catherine, Maidakinsa.
Sai dai ba a shirya wa Shugaban Kasar Liyafar Cin Abincin Rana kamar yadda aka sab aba, saboda yana azumi.
Manufar Ziyarar
Da yammacin Laraba Shugaba Tinubu da Sarki Charles za su gabatar da jawabai yayain wata liyafar cin abincin dare wadda shugabannin siyasa da fitattun mutane masu alaka da Najeriya za su halarta.
A cewar Ministan Yada Labarai na Najeriya, Mohammed Idris, manufar wannan ziyara ita ce “sabunta wata dadaddiyar alaka zuwa kawance na zamani ta fuskar tattalin arziki….
“Sauye-sauyen tattalin arzikin da Najeriya ke yi sun bude kasuwa mafi girma a Afirka, kuma Burtaniya Babbar kawa ce a mataki na gaba.
“Don haka wannan ziyara wani mataki na gaba a yunkurin karfafa zumunta ta fuskar cinikayya da hadahadar kudade da kuma tsaro.”

Ranar Talata Shugaba Tinubu da Maidakinsa suka sauka a Ingila don fara ziyarar ta kwana biyu.
Tun da farko a ranar Laraba, Yarima William da Gimbiya Catherine sun ziyarce su a wurin shakatawa na Fairmont Windsor Park, sannan suka raka su cikin gari, inda Sarki Cahrles da Sarauniya Camilla suke jiran su.
Daga nan ne aka dauki bakin a keken doki zuwa Fadar Windsor, inda aka yi hawan daba da faretin girmamawa, sannan ’yan badujala na Grenadier suka rera taken Najeriya da na Burtaniya.
Bugu da kari, Shugaba Tinubu ya kewaya inda ya duba sojoji, Sarki Charles na biye da shi.
