Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 19 ga Maris da Juma’a 20 ga Maris, 2026 a matsayin ranakun hutun ƙasa domin bikin Ƙaramar Sallah (Eid-ul-Fitr).

Sanarwar ta fito ne ta bakin Babbar Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani, wadda ta ce Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayar da umarnin ayyana hutun a madadin Gwamnatin Tarayya.

Ministan ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan, inda ya buƙace su da su ci gaba da riƙe kyawawan ɗabi’u da suka koyu a lokacin azumin, ciki har da soyayya, karamci, haƙuri da sadaukarwa.

Haka kuma, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa wajen yi wa ƙasa addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da cigaba mai ɗorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *