Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da wasu tsauraran matakai game da yadda za a gudanar da bukukuwan ƙaramar Sallar wannan shekara, inda ta dakatar da wasu muhimman hawan da aka saba yi shekarun baya.

Wannan mataki ya biyo bayan rahotannin sirri da Gwamnatin ta ce ta samu, waɗanda ke nuni da cewa wasu miyagun mutane na shirin amfani da damar bukukuwan don haddasa hargitsi da tashin hankali a cikin babban birnin jihar.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanya wa hannu, Gwamnati ta fayyace yadda tsarin hawan zai kasance:

* Hawan Idi: Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ne zai jagoranci hawan daga filin sallar Idi na Kofar Mata zuwa Gidan Shettima, sannan ya karkare a Kofar Fatalwa ta Fadar Sarki.

* Hawan Nasarawa: Gwamnati ta amince a yi shi, amma a cikin wani sabon tsari sannan ba a kan dawakai ba.

* Hawan Daushe: An dakatar da wannan babban hawa gaba ɗaya a wannan karon.

* Hawan Fanisau da Dorayi: Su ma an dakatar da su domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa, ko da yake gwamnatinsa na son raya al’adu, amma ba za ta taba zuba ido wasu mutane su dagula zaman lafiyar jihar ba. Tuni dai aka ba hukumomin tsaro umarnin tashi tsaye don tabbatar da cewa kowa ya bi waɗannan dokoki, tare da cafke duk wanda aka samu da yunƙurin ta da zaune tsaye.

Gwamnati ta kuma yi kira ga mazauna Kano da su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa jita-jita a kafofin sada zumunta, sannan su fito su yi shagulgulan Sallah cikin lumana.

Idan ba’a manta ba a makon da ya gabata, sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Bayero ya aikewa rundunar ƴan sandan ƙasarnan takardar neman izinin gudanar da hawan ja ƙaramar sallar bana. Matakin da ya jefa al’ummar jihar cikin ruɗanin wanne ɓangare ne zai gudanar da hawan na bana.

Daga bisani mai baiwa gwamnatin shawara akan masarautu Farfesa Tijjani Muhammad Naniya yayi wa manema labarai ƙarin bayanin cewar a gwmnatance, sarkin Kano na 16 Mallam Muhammadu Sunusj ne zai yi hawan na bana.

Dambarawar masarautar ta kano na ɗaukar sabon salo tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheƙa zuwa APC, jam iyyar da sarki Aminu Ado ke samun goyon bayan ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *