Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar juma’a 20 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Shawwal kuma Ranar Salla Karama a Najeriya.
Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun Wazirin Sakkwato, kuma Shugaban Kwamitin Al’amuran Addini na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta ce wannan mataki ya biyo bayan wani rahoton Kwamitin ne cewa ba a samu sanarwar ganin jinjirin wata ba a fadin kasar nan.
“Kwamitin ba da Shawara a kan Al’amuran Addini na Majalisar Sarkin Musulmi da hadin gwiwar Lwamitin Duban Wata na Kasa bai samu wani rahoton ganin wata ba daga daukacin kwamitocin duban wata da ke tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal na shekarar 1447.
“Don haka Alhamis 19 ga watan Maris, 2026 za ta kasance 30 ga watan Ramadana, 1447”, inji sanarwar.
Tun da farko dai rahotanni sun ce ba a ga jinjirin watan ba a kasar Sadiya, inda a can ma aka ayyana Juma’a a matsayin ranar Sallah Karama.
