‘Yan uwan magidancin da ake zargin matarsa ta kashe shi saboda zai ƙara aure na biyu a Ƙaramar Hukumar Rogo, ta Jihar Kano, sun buƙaci hukumomi da su yi musu adalci.

Abdulkarim Haruna, makusanci kuma wanda yake zaman ɗa ga marigayi Hafisu Gausu, yayin tattaunawa da Blueprint Radio, ya yi zargin rashin hukunta masu aikata irin wannan laifi shi ya sa matsalar yaƙi ci yaƙi ƙarewa.

“Muna neman ayi masa adalci, ayi masai adalci. Wannan shine abinda muke nema bisa wannan rai da aka karɓe masa,” in ji shi.

“Kuma kira ɗaya muke ga hukuma irin wannan abubuwa babu shakka suna faruwa bila adadin kuma ina ganin rashin yin hukunci yana ƙara ta’azzara abubuwan nan da suke faruwa. Hukuma ta daure ta rufe ido ta dinga aiwatar da hukunci don arage faruwar waɗannan abubuwa.”

A cewar Haruna, lamarin ya faru ne ranar Jumma’a, kuma lokacin da suka isa gidan bayan faruwar lamarin, sun ga mamacin a kwance a cikin jini kuma da akwai alamar an dake shi ne akansa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar cewa wacce ake zargin tana hannun ’yan sanda kuma bayanan farko da suka samu sun nuna cewa sun samu rashin jituwa ne saboda yunƙuri da marigayin ya yi na ƙara mata kishiya.

“Yanzu haka tana hannu kuma an fara bincike. An same shi cikin jini, an ɗauke shi an kai shi asibiti a garin Rogo, inda likita ya tabbatar da cewa ya rasu,” in ji Kiyawa.

“Yan uwansa suna zargin matar ce ta yi wannan aika-aika. Ana ci gaba da gudanar da bincike.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *