Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na majalisar, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan a Abuja a ƙarshen mako, lokacin da ya karɓi shugabannin ƙungiyar Grassroots Mobilization Network (GMN), ƙarƙashin jagorancin mai gudanarwarta na ƙasa, Injiniya Sadiq Abubakar Adamu Lwafu.
Lwafu ya ce ƙungiyar ta fara shirin wayar da kan jama’a a faɗin ƙasar domin samun goyon baya ga takarar Atiku a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da kuma kawar da jam’iyyar APC mai mulki ta hanyar zaɓe.
- Uzodimma ya jagoranci gwamnonin APC zuwa rantsar da Oyebanji wa’adi na biyu
- Gwamnatin Sokoto ta ware N10.96bn domin gina hanyoyi 11 a jihar
- ’Yan sandan Kano sun yi alkawarin samar da tsaro mai ƙarfi a zaɓen 2027
Ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jefa ’yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki, ƙaruwar matsalolin tsaro da kuma yanayin siyasar da ya bayyana a matsayin mai tauye ’yancin dimokuraɗiyya.
Lwafu bayyana ADC a matsayin dandalin siyasa da ya haɗa gogaggun ’yan siyasa da mutanen da yake ganin sun himmatu wajen ci gaban ƙasa.
Ya kuma ambaci wasu shugabannin jam’iyyar, ciki har da David Mark, Rotimi Amaechi, Rauf Aregbesola, Aminu Tambuwal da Dino Melaye, a matsayin misalan mutanen da ke cikin jam’iyyar.
Da yake mayar da martani, Ologbondiyan ya zargi gwamnatin Tinubu da fifita wasu yankuna ko ƙungiyoyi wajen naɗe-naɗe da aiwatar da manufofinta, inda ya ce, a ra’ayinsa, Atiku ya bambanta da shugaban ƙasar saboda alaƙoƙinsa da mutane sassa daban-daban na Najeriya, waɗanda ya ce za su taimaka wajen haɗa kan al’umma.
Kakakin kwamitin ADC-PCC ya kuma zargi jam’iyyar APC da amfani da bambance-bambancen ƙabila da addini domin cimma muradun siyasa, maimakon mayar da hankali kan jin daɗin jama’a da haɗin kan ƙasa.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa ’yan Najeriya za su yi amfani da zaɓen da ke tafe wajen nuna ra’ayinsu kan salon mulkin da ake gudanarwa.
Dangane da tattalin arziki, Ologbondiyan ya ce Atiku yana da tsare-tsaren farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, ya kuma bayyana cewa idan Atiku ya zama shugaban ƙasa, gwamnatinsa za ta dawo da tallafin man fetur ta hanyar da ya ce za ta kasance a bayyane kuma za ta taimaka wa talakawa tare da ƙarfafa samar da kayayyaki.
Majalisar yaƙin neman zaɓen ADC ta tabbatar wa ƙungiyar GMN cewa za ta ci gaba da haɗa kai da ƙungiyoyin jama’a da sauran masu ruwa da tsaki waɗanda suke son sauya gwamnati ta hanyar zaɓe, dawo da amincewar jama’a ga shugabanci da kuma sake gina ƙasa.