Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya ce ba ya nadamar tsayawa wa wasu abokai, da abokan aiki da kuma wasu manufofin da ya yi imani da su a lokutan da suka gabata, duk da cewa wasu daga cikin waɗanda ya taɓa tallafa wa na iya yin shiru a halin da yake ciki yanzu.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar 23 ga Satumba, inda ya ce a tsawon rayuwarsa ya yi abin da ya ga ya dace bisa imaninsa, da tarbiyyar Arewa, da ƙa’idodinsa da kuma lamirinsa, ba tare da tsammanin yabo ko sakayya daga waɗanda ya tallafa wa ba.

Ya ce mutanen da ya taɓa tallafa wa suna da ’yancin yin nasu zaɓin a yanzu, ciki har da yin magana ko yin shiru, yana mai cewa ba ya son yin hukunci a kansu saboda yadda suka zaɓi mayar da martani.

Tsohon gwamnan ya ce ƙalubale na iya bayyana ainihin yanayin wasu alaƙa, kuma abubuwan da ya koya a cikin watannin baya na iya sa ya sake duba wasu dangantaka da irin abubuwan da yake tsammani daga mutanen da suke kallonsa a matsayin jagora.

Sai dai El-Rufai ya ce ba ya ɗaukar fansa ko neman sakayya kan duk wani rashin adalci, rashin godiya ko cutarwa da aka yi masa, yana mai cewa zai bar hukuncin hakan ga Allah.

Ya ce abin da ya fi damunsa shi ne ya ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da lamirinsa da kuma Allah.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *