Najeriya da Italiya sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa wajen yaƙin neman tallafin dala biliyan 5 domin samar da kuɗaɗen inganta ilimi a faɗin duniya, ƙarƙashin shirin Global Partnership for Education (GPE).

An bayyana hakan ne a wani babban taro mai taken “Sabon zamani na samar da kuɗaɗen ilimi” da aka gudanar a New York a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ke wakilta a taron, ya ce manufar shirin GPE ta yi daidai da shirin Najeriya na inganta sakamakon ilimi da  ƙara damar samun ilimi da bunƙasa ƙwarewar malamai.

Shettima ya ce gwamnatin Najeriya na kallon ilimi a matsayin jari ga makomar tattalin arziki, da ƙara yawan aiki da kuma wadata da zaman lafiyar al’umma.

Ya ce ta hanyar haɗin gwiwar Najeriya da Bankin Duniya da shirin GPE ƙarƙashin shirin HOPE-EDU, ana sa ran za a kai ga kusan yara miliyan 29 da malamai 500,000 a Najeriya.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce Najeriya na neman ƙarin hanyoyin cikin gida na samar da kuɗaɗen ilimi, ciki har da kudaden da EFCC ta kwato bayan an kammala dukkan hanyoyin doka.

Ya ce Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da duba yiwuwar amfani da wasu kuɗaɗen da ba a nema ba da kuma kudaden da suka dade a asusun bankuna domin tallafa wa NELFUND, bisa tanadin doka.

A wajen taron, Italiya ta yi alkawarin bayar da Yuro miliyan 50 ga shirye-shiryen GPE, yayin da gwamnatoci da masu bayar da tallafi suka yi alkawurran da suka kai ga tallafa wa ilimin akalla yara miliyan 370 a duniya.

Mataimakin Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, da sauran masu ruwa da tsaki sun jaddada muhimmancin ƙara kuɗaɗen ilimi da inganta horo da ƙarfafa malamai, yayin da Malala Yousafzai ta yi kira da a ƙara saka hannun jari wajen ilimin ’yan mata da tabbatar da daidaito a fannin ilimi.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *