Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya sake jaddada ƙudirin rundunar na kare muhimman ababen more rayuwa na makamashi, yana mai cewa tsaron makamashi na daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi tsaron ƙasa.

Shugaban sojin ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 23 ga Satumba, lokacin da Daraktan Gudanarwa kuma Babban Daraktan Renaissance Africa Energy Company Limited, Tony Attah, ya jagoranci tawaga zuwa hedikwatar sojoji da ke Abuja.

Laftanar Janar Shaibu ya ce kare muhimman kadarorin makamashi na da muhimmanci wajen tabbatar da ci gaban masana’antu, da daidaiton tattalin arziki da ci gaban ƙasa.

Ya kuma tabbatar wa kamfanin cewa rundunar za ta ci gaba da bayar da goyon baya wajen kare muhimman ababen more rayuwa da samar da yanayin da ayyukan tattalin arziki za su bunƙasa.

Ya kuma jaddada muhimmancin kyakkyawar alaƙa tsakanin kamfanonin makamashi da al’ummomin da ke karɓar bakuncinsu, yana mai cewa amincewa da tattaunawa da fahimtar moriyar juna na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A nasa jawabin, Tony Attah ya yaba wa jami’ai da sojojin Najeriya bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare ƙasa da muhimman kadarorin tattalin arziki.

Ya kuma ce kamfanin zai ci gaba da tallafa wa tsaron makamashi da bunƙasa ƙwarewar ’yan Najeriya da haɓaka masana’antu a ƙasar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *