Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya marabci aikin gina Cibiyar Koyar da Sana’o’i ta Abuja, wadda za ta lakume dala miliyan 12, yana mai cewa cibiyar za ta taimaka wajen bunƙasa ƙananan da matsakaitan sana’o’i da samar da ayyukan yi da ƙarfafa tattalin arziki.
Gwamnatin Koriya ta Kudu ce ke ɗaukar nauyin aikin ta hannun KOICA, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Najeriya ta SMEDAN da shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na Raya Ƙasa, UNDP.
Ana gina cibiyar ne a Cibiyar Raya Masana’antu ta SMEDAN da ke Idu, Abuja.
- Amurka ta hana shugaban Sudan visa domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya
- Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya samu horon soji — Ministan Tsaro
Cibiyar za ta samar da wuraren aiki da kayan fasaha da horo da tallafin fara sana’a da sauran shirye-shiryen taimaka wa ’yan kasuwa.
A matakin farko, ana sa ran za ta tallafa wa ’yan kasuwa 500 da sabbin sana’o’i 400 da ƙananan da matsakaitan sana’o’i 1,500.
Daga cikin dala miliyan 12 ɗin, dala miliyan 5.9 za a kashe wajen gina cibiyar, yayin da dala miliyan 6.1 za su tafi wajen kayan aiki da shirye-shiryen tallafa wa ’yan kasuwa.
Tinubu ya ce cibiyar za ta kuma bai wa mata da masu nakasa damar cin gajiyar shirye-shiryen, ta hanyar samar da wuraren da suka dace da bukatunsu da kuma wurin kula da ƙananan yara ga mata masu yara.