Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta buƙaci shugabannin addinai a Najeriya su mayar da yaƙi da cin hanci da rashawa cikin muhimman abubuwan da suke koyarwa ga mabiyansu.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce addini na da muhimmiyar rawa wajen gyara ɗabi’a da hana cin hanci tun kafin aikata laifin, yana mai cewa satar dukiyar jama’a na cutar da kowa ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.
- Tinubu ya marabci cibiyar koyar da sana’o’i ta dala miliyan 12 a Abuja
- Rundunar sojin Najeriya ta sake jaddada ƙudirin kare muhimman ababen more rayuwa na makamashi
Olukoyede ya bayyana haka a Abuja yayin taron Majalisar Addinai ta Najeriya, NIREC, inda aka ƙaddamar da sabon littafin koyarwa kan yaƙi da cin hanci da aka tanada domin limamai da fastoci.
Ya ce littafin zai taimaka wa shugabannin addinai wajen amfani da koyarwar Musulunci da Kiristanci wajen ƙarfafa gaskiya, amana da kishin dukiyar jama’a.
Hukumar ta ce yaƙi da cin hanci ba zai iya kasancewa aikin hukumomin gwamnati kaɗai ba, inda ta jaddada buƙatar haɗin gwiwar malamai, da shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki wajen sauya ɗabi’a a cikin al’umma.