Shugaban ƙaramar hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara ya kuɓuta daga hannun ’yan ta’adda bayan watanni biyu a tsare
Shugaban ƙaramar hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Nura Umar Abdullahi, da wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su, sun kuɓuta daga hannun ’yan ta’adda, bayan shafe tsawon lokaci a tsare.
Dakarun Operation Fansan Yamma ne suka karɓi mutanen a safiyar Alhamis, 24 ga Satumba, a yankin ƙaramar hukumar Kaura Namoda, bayan sun kuɓuta daga wurin da ake tsare da su.
- Trump da Xi sun gana a Fadar White House, sun tattauna tsaro da fasahar AI
- Kotu ta soke tikitin Pantami, ta umarci PDP ta sake zaɓen fidda gwani a Gombe.
An sace Nura Umar Abdullahi daga gidansa da ke ƙaramar hukumar Bungudu a watan Yulin 2026.
Rundunar ta ce mutanen sun samu damar kuɓuta ne yayin da dakarunta ke gudanar da wani samame bisa bayanan sirri kan wata maboyar ’yan ta’adda a yankin.
Bayan sun kuɓuta, sojojin sun ba su kariya tare da kwashe su zuwa wani asibitin soji domin duba lafiyarsu,da kuma gudanar da bincike na yau da kullum.
Ɗaya daga cikinsu ya riga ya koma ga iyalansa, yayin da ake shirin haɗa sauran da iyalansu da gwamnatin Jihar Zamfara.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da ayyukan fatattakar ’yan ta’adda a yankin domin kare al’umma da kuma taimakawa wajen kuɓutar da sauran mutanen da ake tsare da su ko waɗanda suka ɓace.
Ta kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen dakile ayyukan ’yan ta’adda.