Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka da China sun samu gagarumin ci gaba kan wasu manyan batutuwan da suka shafi ƙasashen biyu, yayin da ya karɓi takwaransa na China, Xi Jinping, a Fadar White House domin tattaunawa.

Trump ya ce tattaunawar tasu za ta mayar da hankali kan tsaro, fasaha da kuma abin da ya kira “super intelligence”, wato fasahar basirar ɗan Adam ta wucin gadi (AI).

A nasa ɓangaren, Xi Jinping ya jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da China, tare da bayyana fatan cewa za a rika yi wa kamfanonin China adalci wajen gudanar da ayyukansu a Amurka.

Kafin isowar Xi, Trump ya sake bayyana cewa ba ya son a ƙara tsaurara dokokin da suka shafi fasahar AI a Amurka, yana mai cewa yana son a bar harkar yadda take a yanzu.

Taron na zuwa ne yayin da Amurka da China ke tattaunawa kan batutuwan tsaro da fasaha da harkokin tattalin arziki, lamarin da ke ƙara sanya dangantakar manyan ƙasashen biyu cikin kulawar duniya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *