Gwamnatin Jihar Kano ta amince da mayar da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda biyar zuwa manyan asibitoci, a wani mataki da ta ce zai faɗaɗa samun ayyukan kula da lafiya na matakin manyan asibitoci ga al’ummar da ke yankunan da ba su da isassun cibiyoyin lafiya.
Cibiyoyin da aka amince da inganta su zuwa manyan asibitoci wato (General Hospitals) sun haɗa da PHC Garun Malam, Kumbotso, Ghari, Garko da Kachako.
Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarinta na ƙarfafa tsarin kiwon lafiya tare da kusantar da ingantacciyar kulawar lafiya ga al’umma, musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ke fama da ƙarancin ayyukan kiwon lafiya.
- Najeriya na maraba da ƙarin masu zuba jari daga Saudiyya – Muhammad Idris
- ICC ta samu tsohon kwamandan ‘yan tawaye da laifi a jamhuriyyar Congo
Bayan amincewar, Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta kafa wata tawaga da za ta fara ziyartar cibiyoyin domin tantance halin da suke ciki.
Tawagar za ta duba gine-gine, da ma’aikata, da kayan aikin asibiti da sauran abubuwan da ake buƙata domin sauya cibiyoyin zuwa manyan asibitoci.
Hukumar ta ce bayan kammala tantancewar, za a gabatar da rahoto da shawarwari ga gwamnatin jihar kan abubuwan da suka rage da kuma matakan da ake buƙata domin fara cikakken aiki a cibiyoyin.
Ana sa ran matakin zai taimaka wajen rage cunkoso a wasu manyan asibitoci, tare da inganta tsarin tura marasa lafiya daga cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko zuwa na matakin sakandare.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, da Sakataren Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda, sun bayyana amincewar a matsayin wani mataki na ƙara inganta harkar kiwon lafiya da kuma samar da ayyukan lafiya kusa da al’umma.
Cibiyoyin Garun Malam da Kumbotso da Ghari da Garko da Kachako ne za su amfana da matakin, yayin da gwamnatin jihar ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su ƙara inganta samun ingantacciyar kulawar lafiya a matakin al’umma.