An samu ra’ayoyi mabanbanta a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) bayan sanarwar da Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta yi na cewa ta samu wani tsohon kwamandan ‘yan tawaye da laifin aikata laifukan cin zarafin bil’adama guda hudu, ciki har da azabtarwa da tsare mutane ba bisa ka’ida ba.

A ranar Laraba, ICC ta samu Mahamat Said Abdel Kani da laifi, bayan ta ce ya jagoranci duka da azabtar da fursunoni a matsayin shugaban wata fitacciyar cibiyar tsare mutane, a lokacin da kasar ke shiga yakin basasa a shekarar 2013.

Yayin da wasu mazauna babban birnin kasar, Bangui, suka ce sun yi farin ciki da hukuncin, wakilan wadanda aka zalunta sun bayyana rashin gamsuwa saboda kotun ta yi watsi da tuhume-tuhume uku saboda rashin isassun hujjoji.

Ya ce a lokacin da laifukan ke faruwa, samun shaidu da daukar hotuna da tattara wasu hujjoji ya kasance abu mai matukar wahala.

A nasa bangaren, Fernand Mande Njapou, na wata kungiyar fararen hula a CAR, ya ce hukuncin babban abin alfahari ne ga wadanda aka zalunta.

Sai dai ya ce akwai wasu manyan mutane da ke da hannu a rikicin, wadanda har yanzu ba a gurfanar da su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *