Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya kafa sabuwar gwamnatin wucin gadi, yayin da ƙasar ke shirin gudanar da zaɓen ƙasa na farko tun bayan samun ‘yancin kai.
Umarnin da shugaban ya bayar ya kawo ƙarshen tsarin raba madafun iko da aka kafa karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018, wadda ta kawo ƙarshen shekaru na yaƙin basasa.
An kuma rusa majalisun dokoki na ƙasa da jihohi, tare da cire mataimakan shugaban ƙasa da ministoci da wasu shugabanni na hukumomin ƙananan hukumomi daga mukamansu.
Sai dai ofishin shugaban ƙasa, bangaren shari’a da hukumomin tsaro za su ci gaba da aiki.
Umarnin ya ce Salva Kiir zai ci gaba da kasancewa shugaban ƙasa har zuwa lokacin zaɓe da kuma lokacin da sabon shugaban da aka zaɓa zai karɓi mulki.
Matakin ya zo kwana guda bayan majalisar dokokin ƙasar ta amince da sauye-sauye a dokar zaɓe, wadanda suka ba Kiir damar ci gaba da mulki a lokacin shirye-shiryen zaɓen.
Sauye-sauyen sun kuma cire mukaman mataimakan shugaban ƙasa da aka samar karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018.
Wannan na nufin Sudan ta Kudu za ta iya ci gaba da shirye-shiryen zaɓen da aka tsara gudanarwa a ranar 22 ga Disamba, duk da cewa har yanzu ba a kammala kundin tsarin mulki na dindindin ba, ba a gudanar da k sauran ayyukan da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 ta tanada.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana matakin a matsayin wani muhimmin mataki zuwa ga zaɓen farko na ƙasar, amma ta bukaci gwamnati ta tabbatar da samar da yanayin da zai bai wa jama’a damar yin zaɓe da kuma tsayawa takara cikin ‘yanci.
Wasu masu sharhi kuwa sun ce sauye-sauyen dokar na iya bai wa Kiir iko mai yawa, musamman ganin cewa an rusa majalisa da cire mataimakansa.
A gefe guda, babban abokin hamayyar Kiir, Riek Machar, wanda ke jagorantar ƙungiyar SPLM-IO, na ci gaba da kasancewa a tsare a gidansa. Ana tuhumarsa da , da suka haɗa da cin amanar ƙasa da kisan kai, zarge-zargen da ya musanta.
Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryهعھen zaɓen, an ƙara tsaurara matakan tsaro a babban birnin Juba, inda aka ruwaito rufe wasu hanyoyi da kafa shingayen binciken ababen hawa a kusa da gine-ginen gwamnati.