Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta ce za ta ba kwamitin bincike mai zaman kansa cikakken haɗin kai wajen gano gaskiyar abin da ya faru da mutuwar mutane 33 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne, waɗanda suka mutu a hannun rundunar NSCDC ta Jihar Neja.
Kwamandan Janar na NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, ya bayyana cewa hukumar za ta samar da dukkan bayanai da takardu da jami’an da kwamitin ke buƙata domin gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya.
- Dole a ga tasirin kuɗin ƙananan hukumomi a rayuwar jama’a –EFCC
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya koma NDC
Kwamitin mai mutum 10, ƙarƙashin jagorancin tsohon Mataimakin Darakta-Janar na DSS, Jonathan Kure, zai binciki yanayin da ya kai ga mutuwar waɗanda abin ya shafa tare da gabatar da shawarwarin da suka dace.
NSCDC ta ce tana mutunta raɗaɗin iyalan waɗanda suka mutu, tare da jaddada cewa mutunta darajar ɗan Adam, riƙon amana da bin doka sun kasance cikin muhimman abubuwan da hukumar ke da alhakin tabbatarwa.