Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya ƙaddamar da sabon Takardar Tsarin Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, da nufin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana da bin ƙa’idojin aiki a cikin kamfanin.
An ƙaddamar da takardar ne a hedikwatar TCN da ke Maitama, Abuja, yayin da kamfanin ya jaddada cewa manufar tsarin ba wai hana cin hanci kaɗai ba ce, har ma da gina gaskiya da adalci da ƙwarewa da riƙon amana tsakanin ma’aikata.
- NSCDC ta sake jaddada gaskiya da bin doka yayin binciken mutuwar masu haƙar ma’adinai
- Mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC: ‘Ba za mu kare mai laifi ba’
Manajan Daraktan TCN, Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz, wanda Daraktar zartarwa mai kula da ma’aikata da ayyukan kamfani, Abiodun Afolabi-Fadahunsi, ta wakilta, ya buƙaci ma’aikata su fahimci tanade-tanaden tsarin tare da amfani da su wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Jami’ar ICPC da ke kula da sashen ACTU na TCN, Monsurat Ajoke Ifeajika, ta ce tsarin zai taimaka wajen hanawa da ganowa, da bayar da rahoto da kuma ɗaukar mataki kan cin hanci da halayen da suka saɓa ƙa’ida.