Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya ce jihar na ci gaba da samun sauyi yayin da take bikin cika shekaru 39 da kafuwarta, inda ya jaddada cewa gwamnati na mayar da hankali kan tsaro da ilimi da lafiya da noma da samar da ababen more rayuwa.
Radda ya ce shirinsa na “Building Your Future” na mayar da hankali ne wajen kusantar da ayyukan gwamnati ga al’umma da kuma samar da damar ci gaba ga matasa da mata da manoma da ƙananan ’yan kasuwa.
- Mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC: ‘Ba za mu kare mai laifi ba’
- NSCDC ta sake jaddada gaskiya da bin doka yayin binciken mutuwar masu haƙar ma’adinai
Dangane da tsaro, gwamnan ya amince da cewa har yanzu akwai ƙalubale a wasu al’ummomi, amma ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar, ba tare da la’akari da bambancin siyasa, addini ko zamantakewa ba, da su haɗa hannu wajen gina Katsina mai zaman lafiya da tattalin arziki mai ɗorewa.
Gwamnan ya taya al’ummar Katsina da ke gida da ƙasashen waje murnar zagayowar ranar, tare da yabawa al’ummar jihar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban Katsina tsawon shekaru.