Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana amincewar zuba jarin dala miliyan 800 a aikin iskar gas na Ima a matsayin wani muhimmin mataki wajen buɗe damar amfani da albarkatun gas ɗin Najeriya da aka gano tun shekaru sama da 50 da suka wuce.
Aikin, wanda kamfanin AMNI International na Najeriya ke haɓakawa tare da TotalEnergies, ana sa ran zai samar da kusan miliyan 300 na cubic feet na gas a kowace rana idan ya kai matakin samarwa na ƙarshe.
An gano albarkatun gas ɗin Ima a shekarar 1973 a yankunan OML 112 da 117 da ke teku, amma bai samu ci gaba ba tsawon sama da shekaru 50.
- NSCDC ta sake jaddada gaskiya da bin doka yayin binciken mutuwar masu haƙar ma’adinai
- TCN ta ƙaddamar da sabon tsarin yaƙi da cin hanci
Matakin Final Investment Decision da aka sanar a ranar 23 ga Satumba ya buɗe sabon babi ga aikin.
Gwamnatin Tinubu ta ce aikin na daga cikin manyan ayyukan gas da suka kai matakin yanke shawarar zuba jari tun bayan hawansa mulki, kuma ana sa ran zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da ƙara kuɗaɗen shiga da samar da iskar gas ga masana’antu da fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.
Haka kuma, kusan kashi 77 cikin 100 na kuɗin aikin an shirya su ne daga cibiyoyin kuɗi na Najeriya, yayin da ake sa ran kusan kashi 60 cikin 100 na ma’aikatan aikin za su fito daga al’ummomin da ke karɓar aikin a Jihar Rivers.