Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya jaddada kudirin Najeriya na ci gaba da taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya halarci zaman bude taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 (UNGA) da aka gudanar a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York.

Janar Musa ya halarci taron ne tare da Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, wanda ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron kasa da kasa.

Bayan zaman bude taron, Ministan ya kai ziyarar aiki zuwa Sashen Tsaro na Ofishin Jakadancin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.

A yayin ziyarar, Mai Bai wa Jakadancin Najeriya Shawara kan Harkokin Tsaro, Birgediya Janar EA Koleosho, ya yi wa Ministan cikakken bayani kan ayyukan sashen da kuma nauyin da yake gudanarwa.

A cewar wata sanarwa da mai taimaka wa Ministan Tsaro kan harkokin yada labarai, Leah Katung-Babatunde, ta fitar, Janar Musa ya yaba wa Birgediya Janar Koleosho da tawagarsa bisa kwarewa,da biyayya da jajircewa wajen cika nauyin da aka dora musu.

Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da kudurin dawo da kuma fadada rawar Najeriya a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a matakin kasa da kasa.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin na kokarin farfado da rawar Najeriya a ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a sassa daban-daban na duniya, domin taimakawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *