Ma”aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar sojojin kasar da dama, a yayin kafsawa da wani gungun ‘yan bindiga masu tarin yawa dauke da manyan makamai.
Shafin jaridar Fitilar Nijar ya ruwaito cewa abin ya faru ne a ranar laraba 23 ga watan satumba a gabashin Abalak ta jihar Tilabery inda aka shafe lokaci mai tsawo a na barin wuta.
- Amurka ta hana shugaban Sudan visa domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya
- Shugaban Sudan ta Kudu ya rusa gwamnatin rikon kwarya gabanin zaɓe
- Amurka ta ce a shirye take ta gana da Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Nijar ta fitar tace dakarun Nijar sun yi nasarar kashe gomman ‘yan bindiga, lamarin da ya tilasta maharan tserewa suka nufi wajen arewacin Mali.
Ba a dai bayyana wasu alkalumma takameme ba dangane da yawan askarawan gwamnati da suka rasu a sanadiyar harin ba.
Kwana ɗaya kafin faruwar al’amarin sojojin Nijar sun kwace dabobi masu dimbin yawa daga hannun wasu barayi a karkarar kafin washegari a sake gwabza faɗa da wani ayarin da ya zo da gagarumin shiri a cewar mahukunta