Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya gabatar da shawarar gudanar da tattaunawar majalisun Najeriya da Majalisar Shura ta Saudiyya duk shekara, domin karfafa alakar kasashen biyu.
Ya ce kamata ya yi kungiyar abokantaka ta majalisun Najeriya da Saudiyya ta zama wata muhimmiyar hanya ta inganta hadin gwiwa tsakanin majalisun biyu.
Da yake jawabi a wata liyafar bikin cika shekaru 96 da kafuwar kasar Saudiyya a Abuja ranar Laraba da daddare, Abbas ya ce ana bukatar ziyartar kwamitocin majalisun kasashen biyu, da kuma samar da tsarin aiki na hadin gwiwa kan zuba jari, da ilimi da zirga-zirgar jiragen sama.
- Najeriya na maraba da ƙarin masu zuba jari daga Saudiyya – Muhammad Idris
- UNGA 81: Shettima zai gabatar da matsayin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya
Ya kuma nemi kungiyar ta rika shirya tarukan ‘yan kasuwa da masana, tare da bibiyar yadda ake aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin kasashen.
Shugaban majalisa ya kuma bukaci Saudiyya ta yi la’akari da bai wa wasu ‘yan Najeriya damar samun biza cikin sauki, bisa la’akari da irin manufar Najeriya ta ba wasu ‘yan Saudiyya damar samun bisa domin bukatar ta shafi ‘yan kasuwar Najeriya,da masu zuba jari da malamai da masu bincike da matafiya masu harkokin kasuwanci da masu rike da fasfo din diflomasiyya.
Ya ce Najeriya da Saudiyya suna da dadaddiyar alaka da ta samo asali daga addini da abota da kasuwanci da al’adu, tare da hadin gwiwa a Majalisar Dinkin Duniya, da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) da OPEC.

Abbas ya ce kasancewar Najeriya na da mafi yawan Musulmi a Afirka, kuma ita ce ta biyar a duniya bayan Indonesia, da Pakistan, da India da Bangladesh, ya ba alakar kasashen biyu muhimmiyar ma’ana ta dan Adam da ta addini.
Game da zirga-zirgar jiragen sama, Abbas ya ce Najeriya na maraba da shirin kamfanin Saudia na fara jigilar fasinjoji kai tsaye tsakanin Jeddah da Abuja daga ranar 1 ga Disamba 2026.
Ya ce jadawalin ya tanadi jirage uku a mako, a ranakun Talata, da Alhamis da Lahadi, tare da bukatar a tabbatar da shirin da wuri, a kara yawan jirage zuwa Legas, a samar da farashi mai sauki, sannan a karfafa safarar kaya.
Dangane da ilimi, Shubaban Majalisar ya yaba da tallafin karatu da Saudiyya ke bai wa daliban Najeriya, yana neman a kara yawan guraben karatun a fannoni kamar likitanci, da injiniya, da fasahar kere-kere ta AI, da makamashi mai sabuntawa, da noma da hakar ma’adinai.
Ya kuma nemi a fadada shirin zuwa binciken digiri na gaba da hadin gwiwa tsakanin jami’o’in Najeriya da Saudiyya, tare da ba mata da daliban da ba su da karfin tattalin arziki damar samun gurabe cikin adalci.

A kan aikin Hajji na shekarar 2026, Abbas ya yaba da yadda aka inganta gudanar da aikin, inda ya ce Najeriya ta kammala jigilar mahajjata zuwa kasar Saudiyya ta jirage 98 cikin kwanaki 18, a kan lokacin da Saudiyya ta kayyade.
Ya ce ya kamata a kara inganta hakan ta hanyar fara shirye-shirye tun da wuri, fayyace farashi, inganta tsarin dijital da karfafa tallafin lafiya da na jakadanci, tare da samar da dindindin na hadin gwiwar Najeriya da Saudiyya kan harkokin jiragen sama, shige da fice, lafiya, masauki da jin dadin mahajjata.