Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya jagoranci tawagar ƙasar a taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, UNGA 81, da aka gudanar a New York, Amurka.
Shettima ya bar Abuja ranar 20 ga Satumba bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya wakilci Najeriya a taron na shekara-shekara da ke haɗa shugabannin ƙasashe da sauran manyan masu ruwa da tsaki na duniya.
A yayin taron, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya gabatar da jawabin Najeriya a babban taron, inda ƙasar ta sake yin kira da a yi garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da bai wa Afirka damar samun kujerun dindindin.
- Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu na cikin ƙoshin lafiya, zai dawo Najeriya
- FRSC ta ce ɗaukar kaya fiye da kima barazana ce ga rayuka da hanyoyin Najeriya
Najeriya ta kuma nemi ingantaccen tsarin tallafin kuɗaɗen ci gaba da ƙarin tallafin yaƙi da sauyin yanayi.
Shettima ya kuma halarci taron manyan ƙasashe kan dabarun sarrafa albarkatun ma’adinan Afirka, inda ya gabatar da matsayin Shugaba Tinubu na cewa ya kamata ƙasashen Afirka su daina dogaro da fitar da ma’adinai ɗanye kawai, su mayar da hankali kan sarrafawa, masana’antu da ƙara darajar albarkatun cikin gida.
A wani taron da Najeriya da Italiya suka haɗa kan samar da kuɗaɗen ilimi, Shettima ya jaddada muhimmancin ilimi wajen bunƙasa ƙwarewar jama’a da tattalin arziki, tare da nuna goyon bayan Najeriya ga shirin Global Partnership for Education na neman dala biliyan biyar domin tallafa wa ilimi.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma gana da ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, inda ya bayyana muhimmancin gudummawarsu ta fuskar zuba jari, da ƙwarewa da hanyoyin haɗin gwiwa wajen ci gaban Najeriya.
Ya kuma gana da sabuwar jagorancin Hukumar ECOWAS da Mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J. Mohammed.
A cewar sanarwar Fadar Shugaban Ƙasa, Shettima ya kuma gabatar da matsayen Najeriya kan kuɗaɗen ci gaba, haɗin kan yankin Afirka ta Yamma, da tattalin arziki, da fasaha, da zaman lafiya da tsaro, tare da sake jaddada buƙatar samar da tsarin duniya mai wakilci da adalci.