Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya tambayi inda Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, yake, bayan Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, UNGA 81, a New York.
Obi ya ce rashin halartar Tinubu a taron ya dasa ayar tambaya, musamman ganin cewa Najeriya ce ƙasa mafi yawan jama’a a Afirka, inda ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya kamata ya kasance cikin waɗanda ke wakiltar muradun Najeriya da Afirka a irin waɗannan manyan tarukan duniya.
A cewar Obi, rashin halartar Tinubu a UNGA na bana ya ƙara kasancewa cikin abin da ya kira rashin bayyana Najeriya kai tsaye a manyan tarukan duniya, yana mai cewa wannan shi ne karo na uku a jere da shugaban bai halarci taron ba, ya kuma tambayi dalilin rashin halartar Shugaban a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubale na cikin gida da na ƙasa da ƙasa.
- FRSC ta ce ɗaukar kaya fiye da kima barazana ce ga rayuka da hanyoyin Najeriya
- NEMA ta ce a nisanta masana’antun gas daga wuraren zama bayan gobarar Kubwa
Sai dai Vice President Kashim Shettima ya halarci taron a matsayin wakilin Tinubu, tare da jagorantar tawagar Najeriya.
A yayin taron, Shettima ya gabatar da jawabin ƙasar a madadin Shugaban, inda ya gabatar da matsayinta kan gyaran tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya, da ci gaba mai ɗorewa, da zaman lafiya da tsaro, da sauyin yanayi da kuma samar da tsarin tattalin arzikin duniya mai adalci.
A gefe guda, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu yana ci gaba da gudanar da aikinsa daga Turai yayin da yake hutun aiki.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ba ya bukatar kasancewa a Abuja a zahiri domin gudanar da ayyukan ofishinsa, yana mai cewa Shugaban na ci gaba da gudanar da tarurruka da masu zuba jari a Faransa.
Fadar ta kuma ce Tinubu zai dawo Najeriya a cikin makon, yayin da rahotanni suka ce an sauya jadawalin dawowarsa daga lokacin da aka fara sanarwa.
Obi ya kammala bayaninsa da kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa Shugaban addu’a domin dawowarsa da kuma samun jagoranci wajen tunkarar ƙalubalen ƙasar.