Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ƙara ƙarfafa imani, haɗin kai da goyon bayan jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.

Janar Musa ya yi wannan kiran ne a yayin ibadar coci ta ƙasa da ƙasa da aka gudanar a National Christian Centre da ke Abuja domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.

Ministan, wanda ya gabatar da karatun farko na Littafi Mai Tsarki a wajen ibadar, ya ce fatan samun Najeriya mai zaman lafiya, da tsaro da wadata ya kasance mai ƙarfi, yana mai jaddada cewa tsaro ba aikin sojoji da jami’an tsaro kaɗai ba ne.

Ya ce tsaro shi ne ginshiƙin da ake gina haɗin kan ƙasa da ci gaban tattalin arziki a kai, tare da tabbatar da cewa Rundunar Sojin Najeriya na ci gaba da kare ikon ƙasar da kuma ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a sassan Najeriya.

A nasa ɓangaren, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi addu’ar samun zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar, yayin da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya jaddada muhimmancin zaman lafiyar dimokuraɗiyya yayin da Najeriya ke tunkarar zaɓen 2027.

Akume ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan tsarin dimokuraɗiyya, yana mai cewa zaman lafiya da haɗin kai su ne ginshiƙan dorewar tsarin.

Bikin, wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, da shugabannin hukumomin tsaro, da jami’an diflomasiyya da malaman addini, ya ƙare da yanke kek ɗin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *