Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA, ta jagoranci aikin ceto da kashe gobara bayan tashin gobara a wata masana’antar gas da ke cikin yankin Kubwa, da ke Abuja.
Gobara ta tashi da misalin ƙarfe 6:20 na safiyar Lahadi, 27 ga Satumba 2026, inda NEMA ta karɓi kiran gaggawa tare da tura ƙungiyoyin agaji, ciki har da jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya.
An shawo kan gobarar da misalin ƙarfe 7:45 na safe, sannan aka jika wurin da ruwa domin rage yiwuwar sake barkewar wuta ko wani fashewa.
- Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta fara neman direban da ya haddasa tashin gobara a Kubwa
- Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu na cikin ƙoshin lafiya, zai dawo Najeriya
NEMA ta ce ba a samu asarar rai ba, sai dai wata mota ta ƙone ƙurmus, yayin da gobarar ta yi wa wasu gine-ginen da ke kusa mummunar illa.
Bayan kammala aikin da misalin ƙarfe 8:45 na safe, jami’in DSAR, a madadin Darakta-Janar na NEMA, ya yaba wa hukumomin da suka shiga aikin bisa gaggawar da suka yi wajen tunkarar lamarin.
Sai dai NEMA ta yi kira ga hukumomin da ke da alhakin sanya ido kan masana’antun gas da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa ana kafa irin waɗannan wurare ne bisa ƙa’idojin tsaro, kuma a nisanta su daga wuraren zama domin rage haɗarin aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.