Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 33 bisa zargin kashe kishiyarta mai shekaru 43 a wani lamari na cikin gida da ya faru a rukunin gidanjin Tafawa Balewa Housing Estate da ke Bauchi.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:05 na yammacin ranar Lahadi, 27 ga Satumba, bayan samun bayanan sirri kan rikici tsakanin matan biyu da ke zaune a gidan mijinsu.
A cewar binciken farko na ’yan sanda, wadda ake zargin, ta ɗauki turmi ta bugi kishiyarta, a goshi, lamarin da ya sa ta faɗi a sume.
- Ministan Tsaro ya yi kira ga ’yan Najeriya kan imani da haɗin kai
- Ikpeme ya buƙaci Super Eagles ta ƙara ƙaimi yayin karawa da Guinea-Bissau
’Yan sandan C-Division da ke Bauchi sun isa wurin, inda aka kai ta zuwa Asibitin Kwararru na Bauchi domin samun kulawa. Sai dai likita ya tabbatar da rasuwarta, sannan aka ajiye gawarta a ɗakin ajiyar gawa domin gudanar da binciken gawar.
Rundunar ta ce an kama wadda ake zargin, yayin da aka kwato turmin da ake zargin an yi amfani da shi wajen aikata laifin a matsayin shaida.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin tura shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da wanda ake zargin idan binciken ya tabbatar da laifin.
Kwamishinan ya jajanta wa iyalan marigayiyar tare da yin kira ga jama’a da su guji tashin hankalin cikin gida.
Ya kuma shawarci iyalai da su nemi taimakon likita da na zamantakewa cikin lokaci ga duk wani ɗan gida da ke nuna alamun matsalar lafiyar kwakwalwa.