Tun lokacin da Najeriya ta samu ’yancin kai a shekarar 1960, tsarin ilimin ƙasar ya samu sauye-sauye masu yawa, daga tsarin makarantu da ke da iyaka zuwa wani babban tsarin ilimi da ya ƙunshi miliyoyin ɗalibai, da dubban makarantu da cibiyoyin manyan makarantu a sassan ƙasar.
A lokacin samun ’yancin kai, Najeriya na da jami’o’i guda biyar kacal. A matakin firamare ma, bayanai na Bankin Duniya sun nuna cewa daga cikin yara miliyan 9.1 da suka kai shekarun shiga makarantar firamare a wancan lokaci, kusan miliyan 2.8 ne kawai suka kasance a makaranta, wato kimanin kashi 31 cikin 100. A wasu yankuna kuma bambancin damar samun ilimi ya yi matuƙar yawa.
A yau kuwa, damar samun ilimi ta faɗaɗa sosai. Bayanai na Tsarin Bayanan Ilimi na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya na shekarar makaranta ta 2024/2025 sun nuna cewa Najeriya tana da makarantu 230,844, tare da ɗalibai kusan miliyan 39.8 da malamai sama da miliyan 1.18. Wannan ya nuna girman sauyin da tsarin ilimi ya samu idan aka kwatanta da shekarun farko bayan samun ’yancin kai.
- ’Yan sanda sun kama matar aure bisa zargin kashe kishiyarta a Bauchi
- Ministan Tsaro ya yi kira ga ’yan Najeriya kan imani da haɗin kai
Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen shi ne faɗaɗa ilimin bai-daya. Shirin Universal Basic Education, wanda aka ƙaddamar a shekarar 1999, an tsara shi domin ƙara damar samun ilimin bai-daya da kuma inganta ingancin ilimi a faɗin ƙasar. Bayanai na UBEC na shekarar 2022 sun nuna cewa makarantu 171,027 ne aka ƙidaya a ƙarƙashin ilimin bai-daya, yayin da adadin ɗalibai ya kai sama da miliyan 47.
Haka kuma, an samu ƙarin damar samun ilimi ga ’yan mata. Misali, shirin AGILE na Bankin Duniya ya tallafa wa makarantar sakandare ga ’yan mata a jihohi 18, inda zuwa shekarar 2025 sama da ’yan mata miliyan 2.1 suka amfana da ingantattun gine-ginen makarantu, yayin da sama da ’yan mata 466,000 suka samu tallafin karatu.

A fannin inganta yanayin koyarwa ma, gwamnati ta ƙara mayar da hankali kan gine-ginen makarantu, da kayan koyarwa da horar da malamai. Rahoton UBEC na shekarar 2024 ya bayyana ayyukan gina da gyaran makarantu, da samar da kayan koyarwa da horar da malamai da jami’an ilimi a matsayin wasu daga cikin matakan da aka ɗauka domin inganta damar samun ilimi da sakamakon koyo.
Sai dai duk da wannan ci gaba, akwai manyan gibi da har yanzu suke buƙatar kulawa. Sabbin bayanan Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya sun nuna cewa duk da yawan ɗalibai da makarantu, matsakaicin adadin ɗalibai ga aji guda ya kai 60.1, fiye da ma’aunin 35 da aka gindaya a ƙarƙashin ka’idojin Universal Basic Education. Adadin ɗalibai ga bandaki ma ya kai 65.9, idan aka kwatanta da ma’aunin 30.

UNESCO ma ta nuna cewa ƙalubalen ilimi a yankin Afirka kudu da Sahara na ci gaba da kasancewa babba, inda kusan kashi 29 cikin 100 na matasa ne ke kammala sakandaren, idan aka kwatanta da kashi 62 cikin 100 a duniya. Wannan na nuna cewa ƙara yawan makarantu da ɗalibai kaɗai bai wadatar ba; ingancin ilimi da kammala karatu su ma suna da muhimmanci.
Saboda haka, idan aka tambaya wane ci gaba Najeriya ta samu a fannin ilimi cikin shekaru 66, amsar ita ce an samu gagarumin ci gaba wajen faɗaɗa damar samun ilimi, da ƙaruwar yawan makarantu da ɗalibai, da bunƙasa ilimin bai-daya, da ƙarin damar ilimi ga ’yan mata da kuma ƙarin shirye-shiryen inganta makarantu da malamai.
Amma shekaru 66 bayan samun ’yancin kai, babban abin da ke gaban Najeriya shi ne yadda za a mayar da wannan ci gaba na faɗaɗa damar samun ilimi zuwa ingantaccen ilimi mai samar da ilimi da ƙwarewar da ɗalibai za su iya amfani da ita wajen samun aiki, da ƙirƙirar sana’o’i da taimakawa wajen ci gaban ƙasa.
A ƙarshe, labarin ci gaban ilimin Najeriya ba labari ne na abin da aka samu kawai ba; labari ne na tafiya daga makarantu kaɗan da damar taƙaitacciyar samun ilimi a shekarar 1960 zuwa tsarin da ke koyar da kusan yara da matasa miliyan 40 a yau.
Tambaya a nan: yaya za a tabbatar cewa kowanne yaro ya samu ingantaccen ilimi?