Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, mni, ya karɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, tare da mataimakinsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a Sokoto, Dr Shamsu Haido, a fadarsa da ke Sokoto.

A yayin ziyarar, Sarkin ya yi kira ga ’yan siyasa da su gudanar da harkokin siyasa cikin lumana, su mutunta juna, tare da kare haɗin kan al’umma, inda ya jaddada cewa bai kamata siyasa ta zama hanyar raba kan jama’a ko haifar da ƙiyayya da gaba ba.

Sarkin ya kuma shawarci ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji kalaman batanci, da zagi da duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali ko rikici a cikin al’umma.

Ya ce ’yan siyasa suna da ’yancin gabatar da manufofinsu da neman goyon bayan jama’a, amma ya kamata su yi hakan cikin mutunci, da bisa tanadin doka, tare da girmama sauran ’yan takara da kuma mutanen da ke da ra’ayoyin siyasa daban.

Mai Martaba Sarkin ya ƙara jaddada cewa ya kamata ’yan siyasa su fifita muradun Najeriya da zaman lafiyar ƙasar a kan bambance-bambancen siyasa, yana mai cewa mukaman siyasa na wucin gadi ne, yayin da haɗin kai da zaman lafiya suke da muhimmanci ga ci gaban al’umma.

Ya kuma ce shugabannin siyasa, musamman waɗanda ke neman mukaman gwamnati, suna da alhakin zama abin koyi ga magoya bayansu, tare da tabbatar da cewa yakin neman zaɓe bai zama sanadin rikici ko rarrabuwar kan al’umma ba.

A nasa jawabin, Peter Obi ya nuna godiya ga Sarkin Musulmi bisa karɓar tawagarsa da kuma sauraron bayanan da suka zo da su.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *