ADC ta tantance tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da kuma Mohammed Hayatu-Deen ta kuma wanke su domin su fafata a zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wannan bayanin yana kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Ranar Laraba ne dai mutanen uku suka bayyana a gaban kwamitin tantancewar.

Sanarwar ta kuma ce an tantance jimillar ‘yan takara 513 wadanda aka wanke domin fafatawa a zaben fitar da gwani na Majalisar Wakilai a fadin kasar nan.

Bugu da kari, a cewar sanarwar, an wanke ‘yan takara 109 domin zaben fitar da gwani na ’yan Majalisar Dattawa, yayin da aka tantance aka kuma wanke ’yan takarar gwamna guda 80.

Jam’iyyar ta ce an tsara gudanar da zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa a ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, kamar yadda jadawalin da shugabannin jam’iyyar suka amince da shi ya tanada.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *