Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ’yan APC sun sauya fasalin siyasa a Najeriya da ruwan ƙuri’un da suka yi don tsayar da shi takara a inuwar jam’iyyar a zaben badi.
Shugaban Ƙasar ya faɗi haka ne ranar Lahadi bayan ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben fitar da gwanin da aka gudanar a faɗin ƙasar nan ranar Asabar.
“Na gode muku duka”, inji Shugaba Tinubu, “Kun sauya fagen [siyasar Najeriya] idan aka dubi irin sakamakon da kuka samar.”
- Takarar Shugaban Kasa: ADC ta wanke Atiku, Amaechi, Hayatu-Deen
- 2027: Kotu za ta yanke hukunci a kan takarar Goodluck Jonathan
- Yadda Kwankwaso da Obi suka yi wuf suka yanki katin NDC
An gudanar da zaɓen fitar da gwanin ne dai a dukkan gundumomi 8,809 da ke ƙananan hukumomi 774.
Abokin takarar Tinubu a wannan fafatawa ɗaya ne kacal: jigo a jam’iyyar ta APC kuma ɗan kasuwa Stanley Osifo, wanda ya fito daga Jihar Edo.
Shugaban Kwamitin Zaɓen Fitar da Gwani na Shugaban Ƙasa na APC Anyim Pius Anyim ne ya karanta sakamakon a cibiyar tattara sakamako da ke Babban Dakin Taro na Ƙasa-da-Ƙasa na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
A cewarsa, ’yan jam’iyya 12,643,306 ne suke da rajista a fadin Najeriya, amma wadanda aka tantance don kada kuri’a a zaben fitar da gwanin sun haura miliyan 11.
“Domin wannan zaɓe”, inji Sanata Anyim, “an tantance masu kaɗa ƙuri’a 11,069,756.
“Bayan tantancewar, masu kaɗa ƙuri’a 11,015,665 ne suka jefa ƙuri’unsu; [sannnan] bayan kammala ƙirga ƙuri’un, cikin farin ciki nake sanarwa a madadin kwamitin cewa ‘yan takarar sun samu ƙuri’u kamar haka: Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya samu jimillar ƙuri’u 10,999,162, Mista Stanley Osifo kuma ya samu jimillar ƙuri’u 16,503.”

Daga bisani Tinubu ya karɓi tutar APC da takardar shaidar nasararsa daga hannun Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
A shekarar 2023 ne dai aka zabi Shugaba Tinubu, wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na farko a badi yake kuma fatan yin wa;adi na biyu idan ’yan Najeriya suka zabe shi a 2027.
