Wasu ’yan takarar majalisar dokokin jihohi da suka tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, daga jihohin Zamfara, Plateau, Taraba da Jigawa sun fice daga jam’iyyar zuwa APC, gabanin babban zaɓen 2027.
Tawagar ’yan siyasar ta gana da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, inda suka bayyana matakin komawarsu APC tare da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ajandar Renewed Hope a zaɓen 2027.
Tawagar wadda Dr Princess Aslam Aliyu Gambiyar daga Zamfara ta jagoranta, ta ce sun yanke shawarar barin ADC ne saboda imaninsu cewa gwamnatin Tinubu na da damar ci gaba da tafiyar da ƙasar ƙarƙashin ajandar Renewed Hope.
- Kwamitin binciken mutuwar mutane 37 a hannun NSCDC ya isa Minna
- Sanata Binos Yaroe ya ƙaddamar da asibitin tafi-da-gidanka a Adamawa
- Zaben 2027: Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya umarci jami’ai su kasance a tsaka-tsaki
Yilwatda ya tarbi sabbin mambobin tare da buƙatarsu da su koma mazabunsu da al’ummominsu domin fara aikin wayar da kan jama’a da kuma shiga ayyukan jam’iyyar a matakin ƙasa. Ya kuma ce za a sanar da Shugaba Tinubu game da matakin da suka ɗauka.
Shugaban APC na ƙasa ya kuma ce zai ba da shawarar a duba yiwuwar bai wa wasu daga cikinsu damar taka rawa a ayyukan wayar da kan jama’a a jihohinsu yayin da ake shirye-shiryen zaɓen 2027.
A yayin ganawar, Yilwatda ya kuma yi magana kan wasu manyan ayyukan raya ababen more rayuwa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a Arewa, ciki har da sassan hanyar Abuja–Kano–Maiduguri, Jos–Akwanga, Kwara–Niger, Sokoto–Kebbi da Kano–Daura.
Ya kuma kare wasu daga cikin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, musamman cire tallafin man fetur, yana mai cewa komawa tsarin tallafin da aka soke na iya shafar kuɗaɗen da ake warewa ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen gwamnati.
Komawar ’yan takarar daga ADC zuwa APC na daga cikin sauye-sauyen siyasa da ake gani yayin da jam’iyyu, da ’yan takara da kungiyoyin siyasa ke sake tsara alaƙoƙinsu gabanin babban zaɓen 2027.