Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci manyan jami’an rundunar da ke jagorantar ayyukan tsaro a jihar da su kasance a tsaka-tsaki, da nuna ƙwarewa tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam yayin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Kwamishinan ya bayar da umarnin ne a yayin wata lacca ta musamman kan kula da tsaron zaɓe da ya shirya wa manyan jami’an rundunar a Kano.
Taron da aka gudanar a Police Officers’ Mess da ke Bompai, da ke Kano, ya samu halartar kwamandojin yankuna, da jami’an ’yan sanda na sassan ƙananan hukumomi, da shugabannin rundunonin dabarun yaƙi da sauran manyan jami’an rundunar.
- Najeriya a shekaru 66: Wane ci gaba aka samu a fannin ilimi?
- Sultan ya yi kira ga ’yan siyasa su guji kalaman da za su jawo rikici a tsakaninsu
- Kwamitin binciken mutuwar mutane 37 a hannun NSCDC ya isa Minna
CP Bakori ya buƙace su da su guji shiga harkokin siyasa ko nuna goyon baya ga kowace jam’iyya ko ɗan takara yayin gudanar da ayyukansu.
Ya ce rundunar ’yan sandan Najeriya na da alhakin kundin tsarin mulki na samar da yanayi na adalci da daidaito ga dukkan jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki a zaɓe.
Kwamishinan ya kuma yi gargaɗin cewa duk jami’in da aka samu yana shiga harkokin siyasa ko kuma ya yi amfani da matsayinsa wajen lalata mutuncin tsarin zaɓe zai fuskanci matakin ladabtarwa.
Ya buƙaci jami’an su gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa, su mutunta haƙƙin ɗan Adam da bin doka, tare da amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwar al’umma wajen gano abubuwan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya.
CP Bakori ya ce amincewar jama’a ita ce ginshiƙin ingantaccen aikin ’yan sanda, don haka ya buƙaci jami’an da su ƙara ƙarfafa alaƙarsu da al’umma domin taimakawa wajen gudanar da zaɓe cikin lumana da tsaro.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta ta samar da isasshen tsaro kafin, da lokacin da kuma bayan babban zaɓen 2027.
Ta kuma yi kira ga mazauna jihar, da jam’iyyun siyasa, da ’yan takara da magoya bayansu da su gudanar da harkokin siyasa cikin lumana tare da bin tanade-tanaden dokar zaɓe, tana mai cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ba.